Yadda Aka Sace Dalibai Da Malaman Sakandiren Kagara

Wani mazauni da ya shaida yadda aka sace dalibai 27 da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati 15, Kagara da ke cikin Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja, ya bayyana yadda masu garkuwar suka daure wadanda suka sace su bibbiyu suka tafi da su.

Mutumin, wanda ke zaune kusa da makarantar, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa ‘yan fashin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, sun far wa makarantar da karfe 2 na dare.

 

Majiyar Legit.ng Hausa ta lura cewa gine-gine da yawa da suka hada da azuzuwa da dakunan kwanan dalibai sun lalace.

 

Majiyar, wacce ta bayyana yadda lamarin ya faru, ta bayyana cewa kafin su koma GSS Kagara, ‘yan fashin sun ajiye babura kusa da makarantar Sakandiren Attahiru, mai nisan kilomita daya zuwa GSS Kagara.

 

Ya ce, “Lokacin da (wadanda aka kwashe din) aka dauke su, sai na ga an daure su biyu-biyu sannan suka doshi inda aka ajiye babura daga inda aka dauke su zuwa daji.”

 

Wani ma’aikacin makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa majiya cewa ‘yan bindigar sun shiga makarantar ne daga baya, inda shingen ya fadi.

 

A cewarsa, sun nufi rukunin ma’aikata, inda aka yi garkuwa da ma’aikata 15, ciki har da malamai kafin su tafi dakin kwanan dalibai.

 

A cewar wata majiyar Punch , wani babban dalibin makarantar sakandare na aji 3, Bejamin Abila, shine ya ankarar da jama’a lokacin da ‘yan bindigar ke gab da gidan kwanan dalibai cewa an sacesu.

 

“Sun yi awon gaba da dalibai 27 a cikin dakin kwanan dalibai tare da daure dukkanin wadanda aka sace din biyu-biyu kafin su dauke su daga makarantar,” in ji majiyar.

Wata majiyar ta koka da yadda makarantar ta lalace, tana mai cewa tana fuskantar hare-haren ‘yan fashifrom KuryaNg.Com https://ift.tt/3s7YTzS February 19, 2021 at 12:57AM https://kuryang.com

Comments

Popular posts from this blog