MUSHA Dariya LABARIN GAYEN XAMANI

Umar Mb Dan Sarki

MUSHA Dariya LABARIN GAYEN XAMANI

Wata rana wata budurwa taje gidan su kawar ta sai ta hadu da wani gayen xamani !!! Ga yanda hirarsu ta kasance:-
Saurayi:- Salam ‘yan mata ya kike?
Budurwa:- Lapia kalau. Alhamdulillah!
Saurayi:- Can I know ur name plz?
Budurwa:- Ehhmmm Maryam… ! Tana yi tana satar kallon shi da gani yakwanta mata arai !!!
Saurayi:- Inane gidanku?
Budurwa:- Tayi wuf ta nuna gidan Qawar ta,kasantuwar Qawar tata masu kudi ne!
Nan sukai exchanging numbers, kullum zai zo saiya kira ta, dan haka takanshirya ta tafi can gidan Qawar anan suke zance, tayi hakan ne danya dinga mata alkhairi da yawa! Asalin gidansu kam talakawa ne authentic, a hakan suna tare ya dingayi mata kyauta kala kala! Wata ran ba wataran ba sai akayi rashin dace wayar sa ba caji kuma gashi yaxo xance yana kofar gidan; Anan ne ya samu wani yaro yace kai kira min Maryam! Sai yaron yace yau bata zo ba! Saurayi yace daga ina? Yaro kam yace daga gidansu.. !
Saurayi:- Au daman banan bane gidan su? Yaro yai gaba yana cewa zo in kaika gidan su, basu karasa ba ya hange ta tana ta tuyar dankali, ga yara sun yayyabeta Yana karasawa ya tsuguna yace ‘yan mata a bani dankali, tana jin muryar shi ta dago suka hada ido, ta mike ta ruga gida aguje, daman gidan ‘kasa ne, yace ki daina gudu ni tsakani da Allah nake son ki,daga nan ya aika afada ma iyayen ta gobe zai turo a rushe gidan ayi musu ginin xamani!
Haka kuwa akayi bayan kwana 2, sai dai wata sabuwa inji ‘yan caca; Tun ranar da aka rushe gidan babu saurayi
ba labarin shi! ! HAHAHHAHAHAHHAHA
Tambaya anan tsakanin Saurayi da budurwa waya fi iya kwarewa wajen YAUDARA???


from KuryaNg.Com https://ift.tt/3rNQIsj February 14, 2021 at 01:26AM https://kuryang.com

Comments

Popular posts from this blog