Ka rushe kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 babu abinda suke sai satar kudi~PDP ga Buhari

Jam’iyyar PDP ta ce bata ga amfanin kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 ba na gqamnatin tarayya.Tace babu abinda kwamitin yake in banda sanar da yawan mutanen da suka kamu da cutar da wanda suka mutu, sai kuma amfani da wannan yanayi da ake na cutar ana satar kudi.

Tace kamata yayi ace kwamitin ya shiga binciken ya da za’a gano rigakafin cutar kamar yanda sauran kasashen Duniya suke amma hakan ya faskara.

Shafin hutudole ne na ruwaito Sanarwar data fito daga me yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan tace tana kira ga shugaba Buhari ya rusa wanna kwamiti a bar NCDC ta yi yaki da cutar.

Tace kuma ta yi mamakin a cikin kasafin kudin 2021 babu tanadin siyo kayan yaki da cutar tace amma hakan ba abin mamaki bane dan dana gwamnatin ta Buhari babu abinda ta tabukawa ‘yan Najeriya.from KuryaNg.Com https://ift.tt/38SnBgN January 17, 2021 at 09:45AM https://kuryang.com

Comments

Popular posts from this blog