Ba Ashiru Nagoma Kadai Ya kamata Akai Asibiti Ba Harda Aisha Tsamiya ~ Khalid Muazu Izala

A shafin sada zumunta wani bawan Allah mai suna khalid muazu izala ya ce ba Ashiru Nagoma kadai ya cancanta akai asibiti ba a’a harda aisha tsamiya dalilinsa na fadan haka ga abinda yace.

 

“Ance ciwon hauka ya kama Director Ashiru Nagoma, nace idan za’a kaishi wajen magani a hada da Aisha Tsamiya

 

Jiya nake karanta wasu labarai wai Aisha Tsamiya ta fada a cikin wani hira da akayi da ita cewa sama da Maza Biliyan Daya (1 Billion Men) ne sukazo neman aurenta, nace lallai ba’a taba yin ‘ya mace mai farin jinita ba kenan a tarihin duniya baki daya.

 

Kidigga ya nuna cewa yan Nigeria gaba dayanmu mazanmu da matanmu yaranmu da manyanmu mutum Miliyan Dari Biyu ne (200 Million).

 

To kaga kenan population din masu neman auren Aisha Tsamiya ya ninka population din yan Nigeria sau 5.

In other words, adadin wadanda sukazo neman auren Aisha Tsamiya yakai yawan mutanen Kasashen Nigeria, Niger, Cameroon, Chad, Ghana, Togo, Burkinafaso, Kenya, Morocco, Tunisia, Algeria, Ethiopia, Egypt, Congo, Tanzania, Uganda, Sudan, South Africa, Gabon, Libya, Mauritania, Congo, Namibia, Botswana, Mali, Angola, Somalia, Zambia, Mozambique, Zimbabwe, Liberua, Madagascar, Senegal idan an hadasu waje guda.

To ai kaga sai muyi addu’an da ita da Ashiru Nagoma Allah ya basu lafiya.”from KuryaNg.Com https://ift.tt/3ccuf3q January 26, 2021 at 08:40AM https://kuryang.com

Comments

Popular posts from this blog