Tashin Hankali ! Zanga-zanga A Birnin Maiduguri (Hotuna)

 

Yanzu haka dubbanin mutane a birnin Maiduguri na jihar Borno sun fito zanga-zangar lumana don nuna fushinsu akan rushe rundinar SARS da gwamnatin Buhari tayi, suna kira da a dawo da SARS a jihar Borno.

Daga jiya zuwa yau an rufe manyan hanyoyi na jihar Borno da ake zuwa wasu garuruwa saboda yanayi na tsaro sakamakon rushe rundinar SARS da akayi, saboda yawancin direbobi basa bin hanya idan basu ga dakarun SARS suna patrol ba.

 

Matakin rushe SARS ya tayar da hankalin Gwamna Zulum, saboda ya yadda da SARS sosai, duk inda zai je a gururuwan jihar Borno su ke bashi kariya, idan an yi masa harin kwanton bauna su ke sakashi a cikin motarsu na sulke, to yanzu an rushe su

Da alamar gwamna Zulum zai gana da shugaba Buhari akan matakin rushe SARS saboda amfanin da suke yi a jihar Borno

Allah Ka kawo mana mafita na alheri Amin

The post Tashin Hankali ! Zanga-zanga A Birnin Maiduguri (Hotuna) appeared first on HausaLoaded.Com.from HausaLoaded.Com https://ift.tt/3lGdFuj

Comments

Popular posts from this blog

#EndSars: Meet Popular Nigerian Prophet, Jeremiah Omoto Fufeyin who Foresaw these chaos beforehand" -Aproko Africa