Kayiwa Girman Allah ka Dawo Mana Da Rundunar #SARS A Jahar Borno – Sakon Zulum Ga Buhari

 

Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Bagana Umar Zulum (Khadimul Ummah) ya roki Maigirma shugaban ‘yan sandan Nigeria IGP Muhammad Abubakar Adamu da ya taimaka ya kawo rundinar SARS da aka rushe zuwa jihar Borno domin su taimaka wajen yaki da Boko Haram saboda amfaninsu da ya gani a zahiri

Gwamna Zulum yayi wannan rokon ne a yau Talata lokacin da Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Argebesola ya kai masa ziyara a birnin Maiduguri Zulum yace; mu a jihar Borno munga kokarin da SARS sukeyi ta hanyar amfani da karfinsu da jaruntarsu suke yakar Boko Haram da gaske

Mu ba ma goyon bayan kowani irin zalunci da wasu gurbatattun jami’an tsaro kan aikata, amma magana ta gaskiya mu anan jihar Borno kokarin da rundinar SARS suke a bangaren yaki da ta’addanci abune da ba za’a misalta ba

SARS suna yin aiki sosai wajen dawo da zaman lafiya a jihar Borno, sun maye mana gurbin kokarin da sojojin Nigeria suke yi a yaki da Boko Haram, inji Gwamna Zulum

Amma abin takaici saboda a cika wa wasu gurbatattu ‘yan Nigeria burinsu sai akayi watsi da kokarin SARS a jihar Borno aka rushe su

Muna fatan Allah Ya sa masu iko da tsaron Nigeria su amsa masa bukatarsa Amin.
Datti Assalafy ne ya wallafa wannan a shafinsa.

The post Kayiwa Girman Allah ka Dawo Mana Da Rundunar #SARS A Jahar Borno – Sakon Zulum Ga Buhari appeared first on HausaLoaded.Com.from HausaLoaded.Com https://ift.tt/3lHELRJ

Comments

Popular posts from this blog