Kada Kuji Tsoron Fada Min Gaskiya, Sakon Zulum Ga Shugabannin Makarantu A Jihar Borno

 

A jiya Lahadi ne gwamnan jahar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya shirya wani zama da shugabannin makarantu 84 a jahar ta Borno domin sanin irin tsalalolin da wadannn makarantu suke fuskanta domin ganin an gyara su.

 

 

Gwamna Zulum ya roki wadannan malamai da cewa su fada masa gaskiya akan matsalolin da wadannan makarantu suke ciki domin ganin an gyara su. Saboda ta hakane za a gyarawa tareda kuma ha6aka harkar ilimi a jahar ta Borno a cewar sa.

Hakama gwamna Zulum ya kara da cewa “kada malamin da yaji tsoron fada min gaskiya don gudun canza masa wajen aiki, ni mutun ne mai son gaskiya ne, kuma ina rokon ku don girman Allah ku fada min gaskiya akan matsalolin da kuke fuskanta da kuma makarantun ku domin ganin an gyara su”. a cewar gwamna Zulum.

Ubangiji Allah ka albarkaci Arewa da shugabannin irin Zulum wallafar shafin rariya.

The post Kada Kuji Tsoron Fada Min Gaskiya, Sakon Zulum Ga Shugabannin Makarantu A Jihar Borno appeared first on HausaLoaded.Com.from HausaLoaded.Com https://ift.tt/3nDVHut

Comments

Popular posts from this blog

#EndSars: Meet Popular Nigerian Prophet, Jeremiah Omoto Fufeyin who Foresaw these chaos beforehand" -Aproko Africa