INEC ta sanar da ranar zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya

INEC ta sanar da ranar zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta sanar da ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.

Wani babban jami’in hukumar Nick Dazang, ya tabbatar wa BBC da cewa Shugaban na INEC Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

Ya kuma jaddada cewa tuni hukumar ta tsayar da mako na biyu na kowace Fabrairun shekarar zaɓe a matsayin makon da za a rinƙa gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

Sai dai har yanzu hukumar ba ta sanar da ranar da aka tsayar ba doimin gudanar da zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisa ba a ƙasar.

A shekarar 2019 dai, an saka ranar 16 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaɓen shugaban ƙasar, amma saboda wasu dalilai aka ɗaga ranar zaɓen zuwa 23 ga watan Fabrairun.

 

The post INEC ta sanar da ranar zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya appeared first on HausaLoaded.Com.from HausaLoaded.Com https://ift.tt/342wdyW

Comments

Popular posts from this blog