Ina Goyon Bayan Masu Zanga zangar #Endsars ~ Tinubu

Ina Goyon Bayan Masu Zanga zangar #Endsars ~ Tinubu

Jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana goyon bayansa ga masu zanga-zangar SARS inda yace duk wani me goyon bayan Dimokradiyya da kuma doka ba zai ki goyon bayansu ba.

Ya jinjinawa shuwagabannin zanga-zangar inda yace sun yi kokari sosai wajan ganin an yi ta bisa tsari, sannan kuma abinda suke nema abu ne me kyau.

Kamar Yadda shafin Hutudole na ruwaito ya kuma yabawa gwamnatin shugaban kasa,Muhammadu Buhari inda yace matasan su lura gwamnati ta rusa SARS sannan kuma ta amince da bukatun da suka bata. Yace dan hakane yake kira ga matasan su yi hakuri haka su bar gwamnati ta aiwatar da canje-canjen da ta dau alkawari.

 

Yace wasu bata gari sun shiga rigar zanga-zangar da niyyar tana hankula. Saidai ya gargadi matasan da cewa kada fa su canja akala zuwa neman shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka, domin idan suka ce zasu yi haka to babu gwamnatin da zata zura ido akan wannan doke ne ta dauki matakan da suka dace.

 

The post Ina Goyon Bayan Masu Zanga zangar #Endsars ~ Tinubu appeared first on HausaLoaded.Com.

Comments

Popular posts from this blog