Babbar Magana ! Magana Taje Kotu Kes Din su Hamisu Breaker

 

MAWAƘI mai farin jini, Hamisu Breajer Ɗorayi, ya bayyana ce akwai alamun za a je kotu kan batun dukan wani mutum da abokin sa ya yi “tunda wanda aka daka bai haƙura ba,” amma ya ce ba da shi za a yi shari’ar ba.

Breaker ya faɗi haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim a daren jiya.

Idan kun tuna, a jiya wannan mujallar ta kawo maku labarin zuwan Hamisu Breaker da abokin sa ofishin ‘yansanda na MTD a Kano hatsaniyar da ta ɓarke da abokin sa Abdulzahir da wani mai suna Sani Kamal Muhammad bayan da su ka daki motar mutumin a kan hanyar Zoo Road da ke Kano ranar Laraba.

A hirar sa da Fim, mawaƙin ya yi ƙarin bayani kan inda aka kwana a kes ɗin, inda ya ce: “Da man ba da ni ake fan ba, kuma ni na fuskanci cewa an yi hakan ne da nufin wani abu. Ka san idan mutum ya ɗaukaka ba abin da ba zai gani ba. Kuma da na dawo na yi bincike sai na ga ashe ma mutumin ɗan unguwar mu ne na Ɗorayi.

“Kuma tun ranar da mu ka halarci ofishin na ‘yansanda ba mu kwana a can ba. Washegari mu ka kai kan mu.

“Maganar sulhu kuma ai ba ta yiwu ba don shi abokin nawa ya taɓa wanda ya fi ƙarfin sa kuma an yi an yi da shi bai haƙura ba.

“Ga masu kuma cewa Abdulzahir hadimi na ne, gaskiya ba haka ba ne. Shi aboki na ne wanda mu ka taso tun yarinta, kuma in ka gan shi ya na da girman jiki.

“Kuma lokacin ma da hakan ta faru akwai yara na guda biyu wanda mu ke tare da su kuma ba su sa baki ba lokacin da abin ya faru.”

Breaker ya ƙara da cewa, “A ranar, na yi da-na-sanin fita wannan unguwar.

“Na ji kuma wasu mutane a kafafen yaɗa labarai daban-daban na faɗin abin da ba shi ba ne, don ko lokacin da abin ya faru ba kowa a danjar. Sai da hayaniyar ta yi yawa ne mutane su ka ankara ina ba wa mutumin haƙuri, sannan kowa ya ƙaraso, don ba wanda zai iya gaya ma ga yadda abin ya faru.

“A ƙarshe, ina godiya ga masoya na da su ka dinga kira na su na min fatan alkhairi da jaje a kan abin da ya faru.”

The post Babbar Magana ! Magana Taje Kotu Kes Din su Hamisu Breaker appeared first on HausaLoaded.Com.from HausaLoaded.Com https://ift.tt/3j8HuCa

Comments

Popular posts from this blog