AUDIO : Zanga-zanga da fito-na-fito da shugabanni baya kawo Alkhairi – Dr Bashir Aliyu Umar

Taken Huduba: Zanga-Zanga Da Fito-Na-Fito Da Shugabanni Baya Kawo Alkhairi.

Masallatai ba za su rayu ba, ba za a iya bude kasuwanni ba, masu sana’a ba za su samu yin sana’arsu ba, idan wannan al’amari na zanga-zanga da fito na fito da shugabanni ya dore.

Yayin da ake kira ga al’umma da su yi biyayya ga jagorori, to su kuma shugabanni yana da kyau su tsaya su ga sun sauke amanar da aka dora musu.

Maslahar aminci da kwanciyar hankali shi ya fi akan a kawar da masu mulki da fitintinun zanga-zanga.

Shugaba inuwar Allah ne a bayan kasa, mu yawaita addu’a sannan mu dauki matakai, babba a cikin matakan shi ne mu koma ga Allah SWT sannan mu yi bakin kokarinmu wajen gyara kuskure a tsakaninmu.

Annabi ya ce idan kaga ana munkari to ka canja shi da hannunka (masu mulki kenan)

Idan fitina ta barke, masu mulki da masu jan ragamar al’umma ba za su iya

Manzon Allah yace mu nemi tsarin Allah daga fitunu na fili da na boye.

Ana yawaitawa shugabanni addu’a domin idan suka mike abubuwan al’umma za su gyaru kuma za a samu nutsuwa.

Muna kira ga shugabanni da su sani Manzon Allah yace mulki wulakanci ne da kaskanci a ranar Alqiyama.

Sayyadina Umar yana tsoron wata akuya ta bata ta wani daga cikin wadanda yake mulka, ba don komai ba sai don kar Allah ya tambaye shi.

Allah zai ya tambayi shugabanni, muna musu addu’a Allah ya dora su akan daidai.

Muna barranta ga Allah da abubuwan da suke yi na zalunci ba ma tare dasu, amma muna tare da su a abubuwansu na daidai. Kuma muna musu addu’a Allah ya shirye su ya yi riko da hannunsu.

Allah ya daidaita mana al’amuranmu. Amin

Ga audion nan ku saukar a wayoyinku domin saurare

DOWNLOAD MP3

The post AUDIO : Zanga-zanga da fito-na-fito da shugabanni baya kawo Alkhairi – Dr Bashir Aliyu Umar appeared first on HausaLoaded.Com.from HausaLoaded.Com https://ift.tt/37d8H4r

Comments

Popular posts from this blog